EFCC ta haramtawa ofisoshin jakadanci hada-hada da Dalar Amurka

Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ta umarci dukkan ofisoshin jakadanci na Najerika su koma amfani da takardun Naira wajen dukkan hada-hadarsu ta kudi.

Kazalika, EFCC ta haramtawa ofisoshin jakadanci na kasashen ketare dake Najeria amfani da Dalar Amurka wajen hada-hadar kudi a cikin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin wata takarda da hukumar EFCC ta aikewa ministan harkokin kasashen ketare, Ambasada Yusuf Tuggar, a ranar 5 ga watan Afrilu.

Jami’an hukumar yaki da cin hanci, EFCC.

Har ila yau, EFCC ta umarci ofisoshin jakadancin Najeriya Dake kasashen ketare su koma hada-hadar kudade da Nairar Najeriya.

KARANTA: ‘Ku kama shi’: Kotu tayi watsi da bukatar Yahaya Bello

A cewar EFCC, sabuwar dokar zata dakile tare da rage dogaro da Dalar Amurka a harkokin da suka shafi tattalin arzikin Najeriya.

Wasikar, mai dauke da sa hannun shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ta bayyana cewa aiwatar da wannan sabon tsari zai farfado da darajar Naira tare da daga darajarta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories