Mutum na farko da aka yiwa dashen ƙodar alade ya mutu

Kodar aladen ta fito ne daga wani alade kuma an gyara ta ta hanyar kimiyyar sarrafa kwayoyin halitta don cire kwayoyin halittar alade masu cutarwa da kuma kara wasu kwayoyin halittar dan adam don inganta dacewarta ga dan-Adam.

Majiyyaci na farko a duniya da aka yiwa dashen ƙodar alade ya mutu, kimanin watanni biyu bayan aiwatar masa da tiyatar.

A cikin watan Maris, Babban Asibitin Massachusetts dake kasar Amurka ya dasa kodar alade da aka gyara ta hanyar kimiyyar sarrafa dabi’a ko ƙwayoyin halitta zuwa ga wani mutum mai suna Rick Slayman.

Majinyacin(mamacin) mai shekaru 62 a duniya ya sha fama da ciwon ƙoda inda ta kai jallin matakin ƙarshe.

Aikin ya kasance wani muhimmi kuma gagarumin cigaba a kimiyyar dashen ƙoda (xenotransplantation)- dashen gabobin jiki ko sassa ta hanyar amfani da fasahar sarrafa ƙwayoyin halitta daga wani nau’in zuwa wani a matsayin mafitar da zata magance matsalar karancin gabobi ko sassa a duniya, in ji asibitin.

A cewar asibitin, mutuwar Slayman ba ta da alaƙa da dashen ƙodar da aka yi masa.

“Iyalanmu sun yi matukar bakinciki game da mutuwar abun ƙaunar mu Slayman, amma ku yi farin ciki, ku kwan da sanin cewa ya zaburar tare da bawa mutane da yawa ƙwarin gwuiwa,” in ji danginsa aranar Lahadi.

Iyalan Slayman sun kai ziyarar ban girma da yabo ga tawagar likitocin da suka kula da shi.

DUBA WANNAN: Zamu zakulo tare da kakkabe ma’aikata da aka dauka aiki da takardun bogi – FG

“Babban ƙoƙarin da suka yi na jagorantar sabuwar kimiyyar dashen ƙodar ya bawa danginmu ƙarin makonni bakwai tare da Slayman, kuma abubuwan da muka yi a lokacin zasu kasance ababen tunawa a cikin zukatanmu.”

Kodar aladen ta fito ne daga wani alade kuma an gyara ta ta hanyar kimiyyar sarrafa kwayoyin halitta don cire kwayoyin halittar alade masu cutarwa da kuma kara wasu kwayoyin halittar dan adam don inganta dacewarta ga dan-Adam.

Har ila yau, masana kimiyya sun kashe duk wasu ƙwayoyin cuta da suka danganci halittar alade don kawar da duk wani haɗarin kamuwa da cuta a jikin dan adam .

Asibitin ya ce “Mun yi matukar bakin ciki” da mutuwar Slayman.

Ba mu da tabbacin cewa mutuwarsa sakamakon dashen ƙodar da aka yi masa kwanan nan ne,”

“Mr. Slayman zai kasance har abada a matsayin ginshiƙin bege ga marasa lafiya masu yawa a duk fadin duniya, kuma, muna matukar godiya sosai bisa amincewarsa da kuma jajircewarsa wajen ciyar da fannin kimiyyar dashen ƙoda”, a cewar asibitin.

Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa (NAN)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories