ISWAP: Ɗan Mamman Albarnawy Ya Miƙa Wuya Ga Jami’an Tsaro A Maiduguri

Babban Ɗa ga Mamman Nur Albarnawy wanda ya assasa ƙungiyar Islamic State of West Africa Province (ISWAP), a ranar Lahadin da ta gabata ya mika kansa ga hukumar tsaron farin kaya (NSCDC) a Maiduguri.

Rahotanni sun Tabbatar da cewa Mahmud Mamman Nur Albarnawy Bayan dogon bincike da ya sha a wurin hukumar sun tabbatar da tabbas shi Ɗa ne ga Albarnawy.

Miƙa Wuyan na sa ya faru ne da taimakon jami’an tsaro sakamakon samun labarin da suka yi na ƙudirin miƙa wuyan da yaron ya ke shirin yi da kuma sa hannun kawun sa da ke Gamborin Ngala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories