Kano: Kotu ta daure ‘yan kasuwar canji 17 na tsawon wata shida

'Yan kasuwar canjin da aka gurfanar da suka hada da Ayuba Ibrahim, Idris Saidu, Idris Usman, Shu'aibu Muhammad, Hamisu Iliyasu, da sauran mutane 12 sun amsa laifinsu a gaban kotu.

Wata babbar kotun tarayya dake karkashin jagorancin Jastis Muhammad Nasir Yunusa ta zartar da hukuncin daurin wata shida ga wasu ‘yan kasuwar canjin kudi su goma sha bakwai dake Kano.

Jastis Yunusa ya yankewa mutanen hukuncin tare da basu zabin biyan tara bayan samunsu da laifin gudanar da kasuwancin canjin kudi ba tare da lasisi ba wanda hakan ya saba da sashe na 57(5)(b) na kundin dokokin hada-hadar kudi na shekarar 2020.

An bawa kowannensu zabin zaman gidan yari ko kuma biyan tarar kudi ta Naira dubu hamsin.

Wadanda aka gurfanar da suka hada da Ayuba Ibrahim, Idris Saidu, Idris Usman, Shu’aibu Muhammad, Hamisu Iliyasu, da sauran mutane 12 sun amsa laifinsu a gaban kotu.

DUBA WANNAN: Kano: Abba ya rattaba hannu kan sabuwar dokar ‘gwaji dole’ kafin aure

A makon da ya gabata ne jami’an tsaron hadin gwuiwa da suka hada ‘yan sanda da jami’an DSS suka kai wani samame a kasuwar canjin kudi ta Wapa dake yankin karamar hukumar Fagge.

A yayin samamen, jami’an tsaro sun kama mutanen tare da kwace kudin kasashen ketare da suka hada da Sefa da Rufi a matsayin shaida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories