Har yanzu ban gaji da siyasa ba – Atiku ya yi Magana akan yiwuwar takararsa a 2027

Atiku ya bayyana cewa har yanzu bai gaji da siyasa ba amma kuma hakan ba yana nufin cewa zai zama dan hana ruwa gudu ga matasa masu sha’awar siyasa ko son yin takara ba.

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma tsohon dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce mambobin jam’iyyarsa ne zasu yanke hukunci akan makomar takarar sa a zaben shekarar 2027.

Atiku ya bayyana cewa yanzu ya yi wuri ya ce ko zai tsaya takara ko ba zai tsaya ba a zaben 2027.

Yayin tattaunawarsa da BBC a ranar Juma’a, Atiku ya ce ganawarsa da dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar LP (Labour Party), Peter Obi, a makon da ya gabata tana da alaka da siyasar 2027.

A makon da ya gabata ne WikkiTimes Hausa ta rawaito cewa Peter Obi ya ziyarci Atiku, Sule Lamido, da Saraki a gidajensu a wani yunkuri na neman a hada kai domin tunkarar zaben 2027.

Atiku ya bayyana cewa shi da Obi sun tattauna batutuwa da suka shafi siyasa da kuma yiwuwar kulla hadaka tsakanin jam’iyyun adawa.

Kazalika, ya yi watsi da batun cewa ba zasu iya fitar da dan takarar hadaka a tsakaninsu ba.

KARANTA: Ɓangaren Shari’a Ita Ce Babbar Matsalar Mu a Ƙasar Nan Ba INEC Ba- Peter Obi

A cewar sa, idan jam’iyyar PDP ta yanke hukuncin cewa dan takarar shugaban kasa daga kudu maso arewa zai fito, babu abinda zai hana ya goyi bayan hakan.

“Ai na fada a baya, tun kafin zabe, cewa idan jam’iyyar mu ta yi hukuncin cewa daga kudu maso gabas dan takara zai fito, zamu amince.  Duk hukuncin da jam’iyya ta zartar zamu yi biyayya,” a cewar Atiku.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa har yanzu bai gaji da siyasa ba amma kuma hakan ba yana nufin cewa zai zama dan hana ruwa gudu ga matasa masu sha’awar siyasa ko son yin takara ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories