Hukumar ƙididdiga ta ƙasa NBS ta Ce Adadin matan da ke Cibiyoyin gyaran hali ta Najeriya ya ƙaru da kashi 4.82 cikin 100 a shekarar 2022
Rahoton na kunshe ne a cikin bayanin ƙididdiga na NBS da ta Yi a kan mata da maza a Najeriya na shekarar 2022 da aka fitar a Abuja a yau Laraba.
Rahoton ya nuna cewa, a shekarar 2020, yawan matan da ke tsare a cibiyoyin gyaran hali ta Najeriya ya kai kashi 4.90, amma ya ragu zuwa kashi 4.48 a shekarar 2021,sannan ya kuma sake karuwa zuwa kashi 4.82 cikin 100 a shekarar 2022.
Bayanai sun nuna cewa yawanci waɗanda aka kama laifin sata shi ne abinda aka fi tuhumar su da shi.