Sabon tsari: CBN ya bukaci ‘yan kasuwar canji su sake neman takardar lasisi

Babban bankin kasa (CBN) ya gabatar da sabon tsari ga dukkan rukunin masu kasuwancin canjin kudi (BDCs) dake Najeriya.

Kazalika, CBN ya ce ya sake nazarin jadawalin abubuwan da suka amince ‘yan kasuwar canji su gudanar.

Hakan na nufin dukkan ‘yan canji sai sun sake aika takardun neman sabon laisisi kafin su cigaba da hada-hadar kasuwancinsu na canjin kudi.

A cewar CBN, an cimma wannan matsaya ne bayan kammala tuntubar masu ruwa da tsaki kuma sabon tsarin zai fara aiki daga ranar 3 ga watan Yuni.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da CBN ya fitar ranar Laraba mai dauke da sa hannun Haruna B. Mustafa, darektan harkokin kudi da tsare-tsare.

DUBA WANNAN: Kano: Kotu ta daure ‘yan kasuwar canji 17 na tsawon wata shida

A cikin sanarwar, CBN ya bayyana cewa ya tanadi lasisi da ka’idoji da sharuda ga dukkan rukunin masu kasuwancin canjin kudi a cikin Najeriya.

A saboda haka, wannan sabon tsarin neman lasisi ya shafi hatta masu rike da lasisi a hannunsu kuma akwai tsari da aka yiwa rukuni daban-daban na masu kasuwancin canjin kudi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories