Abinda Sarki Sanusi II ya fadawa shugabannin hukumomin tsaro yayin ganawarsu

Shugabannin hukumomin tsaro sun shaidawa sarki Sanusi cewa an bukaci su tabbatar da an yi biyayya ga umarnin kotu na hana rushe masarautu biyar na jihar Kano.

Bayanai sun samu dangane da yadda ta kasance yayin ganawar sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi, da shugabannin hukumomin tsaro da suke son a bi dokar kotu na hana rushe masarautun Kano guda biyar da gwamnati ta yi.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa shugabannin hukumomin tsaron da suka gana da Sarki Sanusi II akwai kwamishinan ‘yan sanda, darektan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), kwamandar rundunar ‘civil defence’ (NSCDC), da kuma kwamandar rundunar sojoji.

A cewar Daily Trust, shugabannin hukumomin tsaron sun yi wata ganawa daban-daban da sarki Sanusi II da kuma Aminu Ado Bayero, sarkin Kano na 15 da gwamnati ta sanar da tube shi.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bawa shugabannin hukumomin tsaro damar ganawa da sarki Sanusi a sirrance.

Shugabannin hukumomin tsaro sun shaidawa sarki Sanusi cewa an bukaci su tabbatar da an yi biyayya ga umarnin kotu na hana rushe masarautu biyar na jihar Kano.

Majiya mai tushe ta tabbatarwa da Daily Trust cewa Sarki Sanusi II ya shaidawa shugabannin hukumomin tsaro cewa bai samu wata takarda daga kotu akan batun dakatar da nadinsa a matsayin sabon sarkin Kano a karo na biyu ba.

KARANTA: Jerin sunayen manyan darektoci 14 da aka sallama daga aiki a CBN

“Sarki Sanusi ya yi magana ta fiye da sa’a guda yayin ganawar ta su, ya fada musu cewa gwamnati ta tabbatar da adalci ne akan rashin adalcin da aka yi masa a baya.

“Ya fada musu cewa bai ga takardar kotun da suke magana a kanta ba tare da bayyana takardar a matsayin rudu na dandalin sada zumunta,” kamar yadda majiyar Daily Trust ta shaida mata.

Tun bayan karbar takardar sake nada shi a matsayin sarkin Kano na 16 a ranar Juma’a, sarki Sanusi II ya bayyana cewa dawowarsa karagar mulki ta sake tabbatar da cewa babu mai iya canja abinda Allah ya kaddara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories