Sanata Abdul Ningi ya koma majalisar dattijai bayan wata biyu da dakatarwa

A ranar 12 ga watan Maris majalisar dattijai ta dakatar da Sanata Abdul Ningi na tsawon wata uku bayan ya yi zargin cewa an yi arangizon tiriliyan uku a kasafin kudin shekarar 2024 da Bola Tinubu ya gabatar

Majalisar dattijai a karkashin jagorancin shugabanta, Sanata Godswill Akpabio, ta yafewa Sanata Abdul Ahmed Ningi tare da dawo da shi majalisa.

A ranar 12 ga watan Maris, 2024, majalisar dattijai ta dakatar da Sanata Abdul Ningi, mai wakiltar jihar Bauchi ta tsakiya, bayan ya yi zargin cewa an yi arangizon tiriliyan uku a kasafin kudin shekarar 2024.

Gidan talabijin na ‘Channels’ ya rawaito cewa Sanata Abba Moro na jam’iyyar PDP daga jihar Benue shine ya gabatar da kudirin neman majalisar ta yafewa Sanata Abdul Ningi.

Sanata Abba Moro, wanda ya samu goyon bayan wasu mambobin majalisar, ya bayyana cewa akwai bukatar Sanata Abdul Ningi ya dawo zauren majalisar domin cigaba da aikinsa na wakilci.

DUBA WANNAN: Dan majalisar wakilai daga jihar Abia ya Musulunta, ya sauya sunansa

Kazalika, Sanata Abba Moro ya bayyana takaici da nadama na abinda ya faru amadadin Sanata Abdul Ningi.

Da yake amincewa da kudurin Sanata Abba Moro, Sanata Akpabio ya bayyana cewa bukatar dawo da Sanata Abdul Ningi ta fi karfin batun kabilanci ko na banbanci addini.

Sanata Akpabio ya bayyana Abdul Ningi a matsayin mamba mai tasiri a zauren majalisar dattijai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories