EFCC ta fara binciken Kwankwaso kan badakalar N2.5bn

Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ta fara binciken yadda jam’iyyar NNPP ta kashe kudin yakin neman zaben 2023 da ya gabata.

Binciken na EFCC zai mayar da hankali a kan binciken yadda kwamitin gudanarwa na jam’iyyar NNPP a karkashin dan takarar ta na shugaban kasa, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya sarrafa kudin yakin neman zaben shugaban kasa da gwamnonin jihohi.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa majiya mai tushe ta sanar da ita cewa EFCC ta gayyaci sakataren jam’iyyar NNPP, Kwamred Oginni Olaposi, domin samun Karin bayanai a kan zargin badakalar da yake yi wa Kwankwaso.

Vanguard ta kara da cewa EFCC tana binciken Kwankwaso da sakatariyar sa, Uwargida Folashade Aliu, wacce ake zargin cewa da ita ya yi amfani a matsayin mazurarin karkatar da kudaden yakin neman zabe a NNPP.

EFCC na zargin cewa Kwankwaso ya yi amfani da Uwargida Folashade wajen karkatar da kudaden da jam’iyyar NNPP ta samu domin yakin neman zabe zuwa wani asusu na sirri da jam’iyyar ta yi amfani da shi domin tattara kudaden da aka bata gudunmawa.

KARANTA: Zan bincika yadda Sarki Sanusi II ya koma kujerarsa amma ni babu hannu na – Kwankwaso

Majiyar Vanguard ta sanar da ita cewa korafin Oginni ya ambaci sunayen masu iko wajen fitar da kudi daga asusun jam’iyyar NNPP da suka hada da Farfesa Rufai Alkali, Abba Kawu, da Dipo Olayokun a cikin wadanda suke da hannu a badakalar.

Oginni ya tabbatarwa da Vanguard cewa tabbas ya amsa gayyatar EFCC a ranar Laraba ta makon jiya domin bayar da Karin muhimman bayanai a kan korafin zargin almundahana da ya aika mata.

Gayyatar Oginni da EFCC ta yi alama ce dake nuna cewa hukumar ta fara bincike akan zargin da ake yi wa Kwankwaso. Abin da ya rage shine gayyatar sa domin kare kansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories