Babban Dan sanda, Abba Kyari ya fito daga gidan yari

An saki dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Abba Kyari, daga gidan yari na Kuje dake birnin tarayya bayan ya shafe shekara biyu da rabi.

An tsare Abba Kyari ne ranar 14 ga watan Fabarairu na shekarar 2022 bayan hukumar yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kama shi bisa zarginsa da hulda da manyan ‘yan safarar kwaya na kasa da kasa.

An gurfanar da Abba Kyari ranar 7 ga watan Maris, 2022, tare da wasu sauran kananan ‘yan sanda guda hudu dake aiki a karkashinsa wanda suka hada da Sunday Ubia, Bawa James, Simon Agiriba, da John Nuhu.

A ranar 22 ga watan Mayu da muka yi bankwana da shi, WikkiTimes Hausa ta rawaito cewa wata babbar kotu dake zamanta a Abuja ta amince zata bayar da belin Abba Kyari, biyo bayan rasuwar mahaifiyarsa.

Alkalin kotun, Jastis Emeka Nwite, ya bukaci Abba Kyari ya ajiye miliyan hamsin da Kuma mai tsaya masa wanda shi ma zai ajiye miliyan hamsin.

KARANTA: Kaduna: Mutane da dama sun rasu sakamakon harin ‘yan bindiga a kasuwa

A cewar alkalin, wanda zai tsayawa Abba Kyari dole ya kasance lauyansa Kuma sai ya ajiye takardar shaidarsa ta zama lauya a wurin magatakardar kotun.

Da yake magana da manema labarai, mai magana da yawun gidajen gyaran hali da ke Abuja, Adamu Duza, ya bayyana cewa Abba Kyari ya cika sharudan belin kuma an sake shi ranar Juma’a, 31 ga watan Mayu.

Kazalika, kotun ta tsayar da ranar 31 ga watan Mayu domin sauraron neman bayar belin Abba Kyari wanda ya fara shigarwa tun ainihi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories