Masu kwacen waya sun kashe hazikin babban soja a Kaduna

Wasu batagari da ke kwacen waya sun kashe wani hazikin babban jami’in soja, Laftanal IM Abubakar Isa, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa gida a Unguwar Sarki dake kwaryar birnin Kaduna.

Lamarin ya faru ne ranar Talata, 5 ga watan Yuni, kamar yadda shafin jaridar Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa dake dandalin sada zumunta na ‘X’ da aka fi sani da ‘Twitter’.

Jama’a da dama da suka tofa albarkacin bakinsu a kan batun kisan babban sojan sun bayyana takaici tare da nuna bacin ransu akan yadda masu kwacen waya ke cin karensu babu babbaka a manyan biranen arewa musamman Kano da Kaduna.

Wasu daga cikin mutanen sun bayyana yadda suka taba yin arangama da masu kwacen waya a sassan jihar Kaduna daban-daban tare da yin kiran a dauki matakin gaggawa domin kawo karshen lamarin.

Daya daga cikin wadanda suka tofa albarkacin bakinsu, Abdullahi Umar Zarma (@Zarmaomar) ya yi kira ga rundunar soji akan ta dauki mataki mai tsanani akan masu kwacen waya da kullum ke kara yawa da karfi a yankin Unguwar Sarki da karkashin gadar Kawo a garin Kaduna.

KARANTA: Amarya ta yi yunkurin gutsure al’aurar ango yana bacci a Kaduna

Wasu kuma da kisan sojan ya fusata sun bukaci jama’ar dake zaune a yankunan da lamarin ya fi tsamari su fara zakulo tare kashe masu kwacen waya tunda ba boyayyu bane a unguwanninsu.

Kazalika, jama’a da dama sun nuna alhini tare da yin addu’ar Allah ya jikan Abubakar ya kuma tona asirin wadanda suka hallaka shi.

Rundunar soji da ta ‘yan sandan jihar Kaduna basu fitar da wani jawabi dangane da faruwar lamarin ba har zuwa lokacin wallafa wannan labarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories