PSC ta saki sunayen mutum 10,000 da aka dauka aikin Dansanda

Hukumar kula da ‘Yansanda (PSC) ta saki jerin sunayen mutane dubu goma da suka samu nasarar samun aiki a rundunar ‘Yansandan Najeriya (NPF), rukunin kananan ‘Yansanda.

PSC ta sanar da cewa kowacce karamar hukuma daga cikin kananan hukumomin Najeriya 774 ta samu wakilci a cikin kunshin mutanen da suka yi nasarar samun aikin.

A wani jawabi da PSC ta fitar ranar Talata ta bakin mai magana da yawun hukumar, Ikechukwu Ani, ya bayyana cewa mutane 1,000 daga cikin 10,000 an daukesu aiki ne a matsayin kwararru na musamman yayin da sauran 9,000 zasu zama gama garin ‘yan sanda.

Shugaban PSC, Solomon Arase, ya ce an yi tankade da rairaya kafin zabar sabbin ma’aikata domin tabbatar da an dauki masu nagarta da zasu inganta aikin Dansanda.

DUBA WANNAN: Kano: Mutumin da ya cinnawa Masallaci wuta ana tsaka da Sallah ya shiga hannu

Arase ya bayyana cewa kowacce karamar hukuma ta samu mutane goma kamar yadda tun kafin a fara neman aikin majalisa ta bayar da shawarar hakan.

Domin sanin ko kana daga cikin wadanda suka samu aikin, ga wadanda suka nema, su danna nan tare da saka lambobin katin zama dan kasa (NIN) domin sanin ko ka dace.

Mutum 171,956 ne suka cike neman shiga aikin Dansanda bayan hukumar PSC ta sanar da cewa za a dauki sabbin kananan ‘Yansanda a cikin watan Fabarairu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories