N60, 000 ta yi yawa a matsayin mafi karancin albashi – Gwamnoni

Gwamnonin jihohi 36 na Najeriya sun yi fatali da batun biyan mafi karancin albashi na N60, 000 da gwamnatin tarayya ta yanke.

Darektar hulda da jama’a da yada labarai a kungiyar gwamnoni (NGF), Hajiya Halimah Salihu, ita ce ta sanar da hakan a cikin wani jawabi da NGF ta fitar ranar Juma’a.

A ranar Litinin din da ta gabata aka tashi da yajin aiki bayan kungiyar kwadago (NLC) ta yi watsi da tayin N60, 000 a matsayin mafi karancin albashi da gwamnatin tarayya ta yi.

A ranar Talata NLC ta sanar da sassauta yajin aikin domin samun damar cigaba da tattaunawa da gwamnati a kan mafi karancin albashin ma’aikata.

Sai dai, gwamnoni sun fito sun bayyana cewa idan har aka amince da biyan N60, 000 a matsayin mafi karancin albashi jihohi da dama ba zasu iya biya ba.

NGF ta bayyana cewa wasu jihohin zasu koma ciyo bashi domin biyan albashi idan gwamnati ta amince da biyan N60, 000 a matsayin mafi karancin albashin ma’aikata.

KARANTA: Dalilai 14 da FG ta bayar kan dagewarta akan mafi karancin albashi na N60,000

A cikin jawabin da NGF ta fitar ta bayyana cewa ta amince da cewa akwai bukatar a Kara albashin ma’aikata tare da nuna tausayawa ga NLC bisa kokarin da suke yi na ganin an karawa ma’aikata albashi.

Gwamnonin sun bayyana cewa sun yi la’akari da abubuwa da dama kafin su cimma matsaya akan cewa ba zasu iya biyan N60, 000 kuma su dore da biyan hakan ba.

A cikin jawabin, gwamnonin sun yi kira ga NLC da su yi la’akari da yanayin tattalin arziki da kuma sauran rukunin ma’aikata wadanda ba na gwamnati ba da kuma bukatar sauran ‘yan kasa da basu dogara da albashi ba.

Gwamnonin sun kara da cewa ba iya biyan albashi ne kadai aikin gwamnati ba, akwai bukatar shimfida aiyukan raya kasa da suke bukatar makudan kudade.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories