Kano: Maƙiya sun daukewa Abba hankali a shekarar sa ta farko – Kwankwaso

Jagoran tafiyar Kwankwasiyya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Rabi’u Musa Kwankwaso, ya zargi ƴan adawa  da yunƙurin yin kutse da kuma karkatar da hankalin gwamnatin Kano na tsawon shekara guda.

 Kwankwaso ya bayyana haka ne a sakamakon ayyana dokar ta-ɓaci kan ilimi da gwamnatin jihar ta Kano ta yi.

Ya ce, “Bari in fara da taya Gwamna murnar wannan rana mai cike da tarihi, ranar da gwamna ke ayyana dokar ta-baci kan ilimi. Mutane da dama sun san cewa gwamna yana aiki duk inda ka zaga zakaga ayyukan sa.

 “Duk da cewa gwamnan ya samu kutse a lamurran gwamnatin sa na kusan shekara guda.Ana gama zaɓe, maƙiyan Jiha su ka kai shi ƙara tun daga Kotun Daukaka Kara har zuwa Kotun Koli. Duk da sun san cewa shi ne ya ci zaɓe.

Readability

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories