Mafi Karancin Albashi: NLC Ta Yi Watsi Da N62,000, Za a koma yajin aiki

Gamayyar kungiyoyin kwadago sun yi watsi da tayin gwamnatin tarayya na biyan N62,000 ko N100,000 a matsayin mafi karancin albashin ma’aikata a Najeriya.

NLC ta kafe a kan bukatar neman gwamnati ta biya ma’aikata N250,000 a matsayin mafi karancin albashi a yayin ganawarsu ta karshe ranar Juma’a.

“Mun riga mun bayyana matsayarmyu,” a cewar Chris Onyeka, mataimakin babban sakataren NLC, yayin hirar da aka yi da shi a wani shirin safe na gidan Talabijin din Channels ranar Litinin.

Ya kara da jaddada cewa NLC ba zata karbi tayin gwamnati na biyan N62,000 ko N100,000 a matsayin mafi karancin albashi ba.

Onyeka ya kara da cewa har yanzu wa’adin sati daya da suka bawa gwamnati yana nan kuma zai kare ne ranar Talata kamar yadda tun farko NLC ta sanar.

DUBA WANNAN: Dalla-dalla: NLC ta fayyace dalilin kayyade N615,000 a matsayin mafi karancin albashi

A makon jiya ne NLC ta sanar da sassauta yajin aikin da ta fara ranar Litinin domin samun damar kammala tattaunawa tare da amincewa a kan mafi karancin albashin ma’aikata.

Onyeka ya bayyana cewa wa’adin da suka bawa gwamnati zai kare ranar Talata, 4 ga watan Yuni, 2024, da misalin karfe 12:00 na dare.

Kazalika, ya sanar da cewa bayan shudewar wa’adin, shugabannin kungiyoyin NLC da TUC zasu kira taro domin tattauna cigaba da yajin aikin da aka fara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories