Babbar Sallah: Aminu Ado Ya Aikawa Hakimai Takardar Gayyatar Hawan Sallah

Aminu Ado Bayero, Sarkin Kano na 15 da gwamnatin jihar Kano ta tube baya bayan nan, ya aika goron gayyatar hawan daba da ake yi da Sallah ga hakimai.

Sanarwar gayyatar na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun babban dan majalisar sarki, Alhaji Abbas Sanusi, Galadiman Kano wacce aka fitar ranar Talatar nan, 11 ga watan Yuni.

A cikin takardar, mai dauke da kwanan watan 10 ga watan Yuni, an umarci hakiman masarautar su zo tare da Dagatansu da dawakai da kuma maroka da makada.

Takardar ta bayyana cewa, “muna munartar dukkan hakiman wannan masarauta su zo tare da dagatansu, tawagar hawa da makada domin gudanar da bikin sallah.

“Kazalika, ana umartar dukkan hakimai su taru a fadar Aminu Ado Bayero dake gidan sarki na Nassarawa a ranar Asabar, 9 ga watan Zhulhijjah 1445 wanda ya yi daidai da 15 ga watan Yuni, da misalin karfe 11 na safe domin karbar umarni na gaba ba tare da bata lokaci ko rashin biyayya ba.

DUBA WANNAN: Abinda Sarki Sanusi II ya fadawa shugabannin hukumomin tsaro yayin ganawarsu

“Bayan zaman fada na ranar, Mai Martaba zai gana da hakimai a fadar gidan sarki na Nassarawa domin yi musu karin haske akan yadda hawan Sallah na wannan shekara zai kasance.”

Sanarwar ta kara da cewa an sanar da shugabannin kananan hukumomi batun gayyatar hakiman domin samun saukin jigilarsu zuwa cikin birnin Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories