Ka Yi Koyi Da Kakan ka: Tijjaniyya Ta Shawarci Sarki Sanusi II Ya Ajiye Sarautar Kano

Shugaban darikar Tijjaniyya na duk duniya, Sheikh Muhammad Mahi Ibrahim Nyass, ya shawarci sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi koyi da Kakansa ta hanyar jingine sarautar Kano da aka mayar da shi kamar yadda sarki Muhammadu Sanusi I ya yi.

Sarki Sanusi II shine shugaban darikar Tijjaniyya a Najeriya. An mayar da shi kujerar sarkin Kano a watan Mayu bayan gwamnatin Kano ta yi gyaran dokar masarautu tare da rushe masarautu biyar na jihar.

Har yanzu ana cigaba da dambarwa a masarautar Kano tsakanin sarkin Kano na 15 da aka tube, Aminu Ado Bayero, da sarki Sanusi II.

Sai dai, Tijjaniyya, a cikin wata wasika mai dauke da sa hannun shugabanta na koli, Nyass, ta bukaci sarki Sanusi II ya bi sahun kakansa wanda ya yi watsi da tayin mayar da shi kujerarsa bayan an tube shi.

Wasikar, mai dauke da kwanan watan 3 ga watan Yuni, an aiko ta daga hedikwatar Tijjaniyya ta duniya da ke Kaolack a kasar Senegal.

KARANTA: Abinda Sarki Sanusi II ya fadawa shugabannin hukumomin tsaro yayin ganawarsu

A cewar Tijjaniyya, sun bukaci Sanusi ya ajiye sarautar ne saboda hatsaniya da cece-kucen da mayar da shi kujerar sarautar Kano ke jawowa wanda suke ganin zai iya taba martaba da kimar darikar su baya ga barazanar da lamarin ke yi ga zaman lafiya a jihar.

An nada sarki Sanusi II a matsayin shugaban darikar Tijjaniyya a hedikwatar su da ke Koalack ta kasar Senegal. Kakan sarki Sanusi II, sarki Sanusi I shine shugaban darikar Tijjaniyya na farko a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories