Gawuna Ya Samu Mukami a Gwamnatin Tinubu

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya nada dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin inuwar jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna, a matsayin shugaban kwamitin gudanarwa na jami’ar Bayero da ke Kano (BUK).

Sauran ‘yan kwamitin gudanarwa na BUK da aka nada tare da Gawuna sun hada da Abubakar Dauda, Nora Alo, Ibrahim Obanikoro da Musa Abbas.

A ranar 18 ga watan Mayu ne shugaba Tinubu ya amince da nadin mutane 555 a matsayin shugabanni da mambobin kwamitin gudanarwa na jami’o’i da sauran manyan makarantun gaba da sakandire na gwamnatin tarayya.

Daga cikin wadanda sunansu ya bayyana a wancan lokacin akwai tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, wanda aka bawa shugaban kwamitin gudanarwa na jami’ar Usman Danfodio da ke Sokoto.

DUBA WANNAN: Sansanin Sojin Amurka da Faransa: Dattijan arewa sun gargadi Tinubu

Sai dai, kwararru sun yi suka akan rashin cancantar wasu daga cikin sunayen da aka gani, lamarin da ya sa Tinubu sake yin kwaskwarima da gyaran fuska ga kunshin sunayen mutanen da ya nada a farko.

A wannan sabon nadin ne sunan Gawuna ya bayyana tare da sauran wasu da dama da shugaba Tinubu ya amince da nadinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories