Sansanin Sojin Amurka da Faransa: Dattijan arewa sun gargadi Tinubu

Tun bayan samun rahotannin cewa kasar Nijar ta umarci sojojin kasashen Amurka dana Faransa su fice mata daga kasa ake yada jita-jitar cewa zasu kafa sabon sansaninsu a Najeriya.

Sai dai, wasu dattijan arewa sun rubutawa shugaban kasa, Bola Tinubu, wasikar gargadin cewa kar ya sake ya bar sojojin kasar Faransa dana Amurka su kafa sansaninsu a Najeriya.

Dattawan da suka rattaba hannu akan wasikar yayin hutun karshen mako sun hada da Farfesa Attahiru Jega na Jami’ar Bayero dake Kano, Kabiru Sulaiman Tsafe na cibiyar bincike da cigaban arewa (ARDP) dake Kaduna, da Abubakar Siddique Mohammed, na cibiyar bincike da horo a siyasa (CEDDART).

Sauran sun hada da Jibrin Ibrahim na cibiyar cigaban siyasa (CDD) dake Abuja, Auwal Musa Rafsanjani na cibiyar CISLAC dake Abuja da kuma Y. Z Ya’u na cibiyar cigaban sarrafa bayanai ta hanyar kimiyya (CITAD).

Dattijan sun bayyana cewa ba boyayyen lamari bane cewa kasashen Amurka da Faransa na kokarin lallaba Najeriya, Togo, Benin da Ghana don su saka hannu akan wata yarjejeniyar tsaro da zata basu damar kafa sansanin soji a kasashen.

Kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso sun kori sojojin kasashen Amurka da Faransa bayan sun shafe shekaru da kafa sansani a kasashensu. Kazalika, sun maye gurbinsu da sojojin kasar Rasha.

“Kasashen sun mayar da wani bangare na sojojinsu da aka kora zuwa kasar Chad. Amma Amurka da Faransa sun nuna kiri-kiri cewa sun fi sha’awar kafa sansanin sojojinsu a Najeriya”.

KARANTA: Zamu zakulo tare da kakkabe ma’aikata da aka dauka aiki da takardun bogi – FG

“Alamu na nuna cewa Najeriya zata iya amincewa da bukatar kasashen wanda hakan ya jefa mutane cikin fargaba saboda zai shafi harkokin tsaro na cikin gida, ” kamar yadda dattijan suka bayyana a cikin wasikar da suka aikewa Tinubu.

Kasashen da suka kori sojojin Amurka da Faransa sun koka cewa kasancewar sojojin a kasashensu bai taimakesu ba ta fuskar tsaro. Hasali ma, sabanin samun saukin aiyukan ta’addanci sai ta’azzara suke kara yi wanda hakan ya haifar da juyin mulkin soji a kasashen.

A baya gwamnatin Amurka tasha yunkurin neman sahalewar gwamnatin Najeriya domin kafa sansanin soji amma hakarta bata cimma ruwa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories