Jihar Zamfara ta fara biyan mafi ƙarancin albashi na N30,000

Hakan ya biyo bayan ganawar da gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya yi da shugabannin kungiyoyin ƙwadago inda ya yi alkawarin fara biyan mafi karancin albashin ma’aikata a watan Yuni.

Ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a ta bakin mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris, ya ce ma’aikatan jihar Zamfara sun fara karbar albashin su ne a ranar 12 ga watan Yuni, gabanin bikin Sallah don kar a barsu a baya wajen nishadin salla babba.

Ya ce kafin yanzu ma’aikatan gwamnati a baya suna karɓar mitsitsin albashi da bai taka kara ya karya ba na Naira 7,000 duk wata, inda ya ce gwamnatinsa ta kudiri aniyar ganin an samu ingantuwar walwalar ma’aikata.

“Gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal, ta biya albashin watan Yuni domin tallafa wa ma’aikata wajen shirye-shiryen bukukuwan Sallah Babba mai zuwa,” a cewar mai Magana da yawun gwamnan.

Ya kara da cewa, “Wannan ya yi daidai da cika alkawarin da gwamnan ya dauka a watan jiya na aiwatar da mafi karancin albashi na N30,000. “

DUBA WANNAN: N60, 000 ta yi yawa a matsayin mafi karancin albashi – Gwamnoni

“A baya, ma’aikatan gwamnati a Zamfara na karɓar mafi karancin albashin da bai haura Naira dubu bakwai ba.

 “Gwamnatin mu ta kasance mai kyautata mu’amala da ma’aikata tun farkon ta, inda ta tabbatar da biyan albashin watanni uku da aka hana, tallafin hutu, basussuka, da biyan albashi duk a kan lokaci.

“Gwamnati za ta ci gaba da ƙoƙarin kawo gyara da kuma farfado da ma’aikatan jihar Zamfara.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories