Luguden wutar NAF Ya Kashe ‘Yan Ta’adda Fiye Da 80 A Katsina

Rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ta ce dakarun sojin sama na Operation Hadarin Daji sun hallaka ‘yan ta’adda fiye da 80 a luguden wutar da ta yi ta sama a baya-bayan nan a ƙauyen Gidan Kare dake unguwar Ruwan Godiya dake karamar hukumar Faskari a jihar Katsina.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar sojin saman Najeriya, AVM Edward Gabkwet, ya fitar a ranar Litinin a Abuja.

Mista Gabkwet ya ce harin da aka kai a daren ranar 15 ga watan Yuni ya yi sanadiyyar mutuwar ‘yan ta’addar tare da kona babura sama da 45.

Ya ce harin ya zama dole ne biyo bayan bayanan sirri da aka samu cewa ‘yan ta’addan da yawansu ya kai 100 sun ƙona gidaje a wani kauye mai tazarar kilomita biyar daga kauyen Gidan Kare.

A cewarsa, da misalin karfe 8:30 na dare, an ga gidaje da dama suna cin wuta tare da ɗaukacin kauyen da aka kai harin.

“Jim kadan, an ga babura 12 suna tashi daga kauyen, suna bin hanyar fita daga kauyen zuwa wani wuri kusa da Kauyen Gidan Kare da sansanin Kuka Shidda, inda suka shiga cikin wata mota tare da adadi mai yawa na ƙungiyar su.

“An kuma ga wasu ‘yan ta’adda sun iso wurin daga bangarori daban-daban, lamarin da ke nuni da cewa wurin ya kasance wata mahaɗa da ‘yan ta’addan ke amfani da ita wajen shirin ƙara kai hare-hare a ƙauyukan da ke kusa da mahaɗar.

“Bayan an gabatar da irin wannan bayanan sirri da ba kasafai ake samun irin su ba, sai dama ta wanzu, sai aka nemi izini, aka samu, nan take aka kai ga gano wurin da misalin karfe 9:40 na dare, ba tare da wata-wata ba aka ƙaddamar da harin, inda aka tabbatar da an kawar da ‘yan ta’adda sama da 80, sannan an ƙone babura kusan 45, yayin da aka ga ‘yan ta’addan da suka tsira suka gudu wasu kuma sun yi mummunar jikkata.

KARANTA: Masu kwacen waya sun kashe hazikin babban soja a Kaduna

 “An samu ƙarin bayanan sirri  da suka tabbatar da cewa ‘yan ta’addan na da alaƙa ƙasurgumi kuma fitaccen shugaban ‘yan ta’adda, Yusuf Yellow da abokin burminsa Rabe Imani.

“Wadannan hare-haren, tare da wasu kafin yanzu, babu shakka sun daƙile ayyukan ta’addanci a yankin,” in ji shi.

Babban hafsan sojin sama Air Marshal Hasan Abubakar ya yabawa irin ƙoƙarin da bangaren sojin sama da sauran jami’an tsaro ke yi na rage ƙarfi da tasirin ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma.

Shugaban ya yi wannan yabon ne a lokacin da yake ƙaddamar da aikin samar da tashar jirgi sansanin gudanarwa na ko ta kwana (213 Forward Operating Base) da ke jihar Katsina a ranar Litinin.

 Ya ce haɗin gwuiwa da taimakekeniya tsakanin hukumomin tsaro da ake yi shine ke kawo nasarorin da bangaren sojin sama ke samu.

Ya kuma buƙaci sauran hukumomin tsaro da su ƙara himmatuwa da jajircewa ba tare da yin ƙasa a gwuiwa ba wajen yaƙi da ta’addanci da duk wani nau’in muggan laifuka a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories