Masarauta: FG Da APC Na Kokarin Kirkirar Sabuwar Boko Haram A Kano – Kwankwaso Ya Koka

Jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar  (NNPP) a shekarar 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, ya zargi Jam’iyyar APC da gwamnatin tarayya da yunƙurin kitsa tarzoma da tada zaune tsaye inda ya danganta hakan da cewa ” tada ƙayar baya ne mai kamanceceniya ko sabon salon Boko Haram” .

Gwamnatin tarayya ta jagoranci yunkurin haifar da sabon salo na ‘yan ta’addan Boko Haram da masu tayar da kayar baya a Arewacin Najeriya.

Kwankwaso dai na mayar da martani ne kan al’amuran da ke faruwa a Kano, inda hukumomin tsaro na tarayya da tsarin mulkin kasar ya dora musu alhakin tabbatar da zaman lafiya da bin doka da oda, ke marawa tsohon Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, baya.

Da yake jawabi a wajen bikin kaddamar da aikin gina titunan karkara mai tsawon kilomita 82 a mahaifarsa ta Kwankwaso, da ke ƙaramar hukumar Madobi, Sanata Kwankwaso ya ce mutanen Kano su yi tir da duk wani yunkuri na kawo cikas ga gwamnatin da aka kafa a jihar.

“Muna da mabiya masu ɗimbin yawa saboda mutane sun yarda da mu, mu masu goyon bayan jama’a ne, kuma gwamnatin NNPP ta ƙudiri aniyar yiwa mutane hidima a duk inda suka zaɓe ta.”

KARANTA: Kotu Ta Haramtawa EFCC Kama Kwankwaso Da Wasu Mutane 6

Sanata Kwankwaso ya kara da cewa “a matsayinmu na ‘yan siyasa ba za mu zuba ido, mu naɗe hannayenmu muna kallon makiyan jihar nan suna ruguza zaman lafiya a jiharmu ba, za mu yi duk mai yiwuwa wajen marawa gwamna baya don samun nasara.”

“Ina farin ciki da hakan bai ɗauke masa hankali ba, kuma bai shagala ba, ya mayar da hankali tare da himmatuwa wajen cimma burinsa na hidimtawa jama’a.”

“Akwai ‘ƴan jhiar Kano, maƙiya jihar, wadanda su ma suna fama da tabin hankali, kuma su ne ke baiwa gwamnatin tarayya shawara kan yadda za ta karɓe Kano cikin gaggawa ta hanyar ayyana dokar ta ɓaci.

“Wannan hauka ne na ajin ƙarshe da mutanen Kano nagari, masu son zaman lafiya, masu kishin ƙasa ba za su lamunta ba.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories