Gobara Ta Lalata Wani Bangare Na Katafaren Shagon Ado Bayero A Kano

Wata gobara da ta tashi da tsakar ranar Laraba ta lalata wani bangare na katafaren shagon siyar da kaya na Ado Bayero (Ado Bayero Mall) da ke kan titin gidan zoo a birnin Kano.

Babban manajan shagon, Elizabeth Adeyemo, ta tabbatar wa da jaridar Punch faruwar lamarin tare da sanar da cewa ma’aikatan hukumar kashe gobara sun bada gudunmawa wajen shawo kan gobarar.

Jaridar Punch ta rawaito cewa an dakatar da jama’a daga shiga babban shagon a yayin da gobarar ta tashi.

DUBA WANNAN: Masarauta: FG Da APC Na Kokarin Kirkirar Sabuwar Boko Haram A Kano – Kwankwaso Ya Koka

A cewar Manajar, an hana jama’a shiga shagon ne saboda ma’aikatan hukumar kashe gobara su samu nutsuwar yin aikinsu. Kazalika, ya ce bai san menene ya haddasa tashin gobarar ba.

Sai dai, rahotanni sun bayyana cewa duk da wutar ta lalata wani bangare na babban shagon, ba a samu asarar rai ko jikkata ba sanadiyyar tashin gobarar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories