Atiku Ya Kaiwa Tsohon Shugaban Ƙasa Buhari Ziyarar Ban Girma A Daura

Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar a yau Asabar ya kai wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyara a mahaifarsa, da ke Daura a jihar Katsina.

 Tsohon mataimakin shugaban kasar ya isa filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’adua dake Katsina da misalin karfe 11:25 na safe inda daga nan ya wuce Daura kai tsaye ya samu ganawa da Buhari.

Da yake zantawa da manema labarai a Katsina tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce ya kai ziyarar ne domin taya shugaban kasar murnar kammala bikin babbar Sallah lafiya.

 Haka kuma Atiku ya ƙi tofa albarkacin bakin sa game kan rikicin shugabancin jam’iyyar PDP na jihar Katsina, inda ya bayyana cewa jama’a su ne za su yanke shukuncin wanda suke so ya jagorance su a babban taron jam’iyyar.

Sai dai masu lura da al’amuran yau da kullum suna ganin cewar ziyarar ba za ta rasa nasaba da shirin da Atiku ke game da fara sake fasalin zaben 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories