Dalilin Da Ya Sa Ban Je Kotu Ba Bayan Ganduje Ya Tube Ni – Sarki Sanusi II

Sarkin Kano, Muhammadu Sansui II, ya yi magana a kan tube shi daga kujerar sarki da tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi a cikin watan Maris na shekarar 2020.

Yayin wata hira da ya yi da jaridar ‘Sun’, Sanusi II, tsohon gwamnan babban bankin kasa (CBN), ya bayyana cewa shi daya ne kawai daga cikin daruruwan ‘yan sarauta da suka fito daga gidan sarautar Kano a saboda haka ba shi kadai ne ya yi gadon zama sarki ba.

Da yake amsa tambaya a kan dalilin da yasa bai garzaya kotu ba bayan Ganduje ya sauke shi daga kujerar Sarki, Sanusi II ya ce, “dalilai da yawa. Na fada muku cewa akwai daruruwan wadanda suka gaji kujerar Sarki. Ni daya ne kawai daga cikinsu.”

“Allah ne ya zabe ni, idan kuma ya kawo lokacin bari na haka zan hakura na tafi saboda Allah ya fini sanin dalilin faruwar hakan.”

“An zargeni da rashin biyayya ga gwamnati kafin a saukeni amma fa ba a taba tuhuma ta da lafin ba kafin daukan wancan mataki na tube rawani na. Kazalika, babu bayani a kan irin rashin biyayyar da ake zargin na aikata, ba a bani dama domin na kare kai na ba.

“A bayyane take gareni cewa gwamnatin tarayya da ta jihar Kano sun yanke shawarar a cire ni,” a cewar Sarki Sanusi II.

KARANTA: Na Fahimci Dalilin Aminu Ado Bayero Na Yin Fushi – Sarki Sanusi II

Sarki Sanusi II ya bayyana cewa koda kotu ta bayar da umarnin a mayar da shi, ba zai koma ba saboda ba zai iya aiki tare da gwamnatin Ganduje ba kuma ba zai yi farinciki ko jin dadin aiki da gwamnatinsa ba.

“To, mu kaddara cewa ma kotu ta ce na koma kujera ta. Kuna tunanin cewa ina son yin aiki da wannan gwamnatin ne? shin zan iya yin aiki da gwamnatin cikin farinciki a matsayina na Sarki? Sarki a karkashin gwamna ya ke. Doka ta bashi iko sama da kai. Idan ya ce ba ya sonka kuma ya nuna maka hakan, idan na cigaba da aiki da shi zai kuntatawa rayuwa ta ne,” kamar yadda Sarki Sanusi ya bayyana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories