Wutar Lantarki Ta Yi Ajalin Ɗalibi Sakamakon Azabtar Da Shi 

Ɗalibi Blaise Felix a makarantar sojin saman Najeriya da ke Mando Kaduna mai shekaru 15 ya gamu da ajalin sa sakamakon azabtar da shi da wasu ƴan uwansa ɗalibai su biyu suka yi a dakin kwanan dalibai da ke makarantar .

Sai dai har yanzu Rundunar sojin saman na Najeriya ba ta bayyana sunan waɗanda suka aikata wannan aika-aikan ba,Hakazalika ba su bayyana Musabbabin mutuwar wannan ɗalibi ba amma ta ce a halin yanzu ana gudanar da kwakkwaran bincike don gano abin da ya yi sanadin mutuwarsa.

Amma dai hukumar makarantar ta yi ƙoƙarin mika wata ‘yar gajeriyar sanarwa da kakakin hukumar NAF, Air Vice Marshal Edward Gabkwet ya fitar a jiya inda sanarwar ke cewa:

   “Shugaban Hafsan Sojan Sama, Air Marshal Hasan Abubakar da ma daukacin iyalan NAF sun yi alhinin rasuwar ɗaya daga cikin dalibanmu a makarantar sakandiren sojojin sama, Kaduna a ranar 19 ga watan Yuni 24.

“Don guje wa jita-jita iri-iri, a halin yanzu ana ci gaba da gudanar da cikakken bincike don gano ainihin abin da ya kai ga mutuwar wannan ɗalibi, kuma wannan lamari mun bashi dukkan kulawa domin ganin an fitar da sakamako da wuri.”

kuma an ajiye gawar a dakin ajiye gawarwaki har zuwa lokacin da za a gama gudanar da bincike

Wani jami’in rundunar sojin sama wanda ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 19 ga watan Yunin 2024.

 Ya ce wasu ɗaliban SS3 guda biyu ne suka gayyaci wanda aka kashen zuwa dakinsu domin hukunta shi wanda hakan ya yi Ajalin sa.

 “Abin da na sani shi ne wasu dalibai biyu ƴan SS3 da suka kammala WAEC kuma suna jiran jarabawar NECO sun gayyaci Felix Aliyu wanda shi ne mataimakin shugaban yara zuwa cikin dakinsu domin hukunta shi.  Sakamakon binciken ya nuna cewa wadannan dalibai biyu sun azabtar da shi ne da suka wanda hakan yayi ajalinsa sakamakon mannja da yayi da gadon Ƙarfe wuta ta ja shi har ya mutu .Amma Da farko mun samu labarin cewa wanda aka kashen wuta ce ta jashi amma daga baya muka tattaro cewa abin ba haka yake ba.  Kashe shi aka yi.Yanzu haka an kama daliban su biyu da ake zargin suna da hannu wajen aikata laifin,” inji shi.

 Da aka tuntubi ƴan uwan mamacin da ta nemi a sakaya sunan ta tabbatar da faruwar lamarin amma ta ce ba tada ikon yin magana da manema labarai.

Shugaban kungiyar iyaye da malamai na makarantar wanda ya wallafa a dandalin WhatsApp na PTA ya ce Felix ya rasu ne sakamakon azabtar da shi da wasu dalibin SS3 suka yi ta hanyar amfani da wutar lantarki a dakin ba bisa ƙa’ida ba wanda sakamakon dukan shi da suke yi jikinsu ya manne da gado wanda wuta ke jiki ya jashi ya kashe shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories