Matakan Kare Kai Daga Kamuwa Da Cutar Kwalara

Kamar yadda aka sani damina ta Kunno Kai wanda shine lokacin da cutuka irin su Kwalara suka fi yaɗuwa a cikin al’umma,Hakan ne ya sa Gwamnatin tarayya ta shawarci ƴan Najeriya da su yi ƙoƙarin tsaftace kansu da kuma muhallin su domin dakile yaɗuwar cutar a faɗin ƙasar.

 Babban Sakatare a Ma’aikatar Muhalli, Mahmud Kambari, shi ne ya yi jawabin a ranar Asabar a wajen wani taron tunawa da ranar tsaftar muhalli ta kasa na shekarar 2024 da aka yi a garin Piwoyi da ke Abuja

 Kamar yadda aka saba Ana gudanar da ranar tsaftar muhalli ta ƙasa a ranar 28 ga watan Yunin kowace shekara domin ganin an wayar da kan ƴak Najeriya game da mahimmancin tsaftar jiki da na muhalli.

 Jawabi ya cigaba da cewa manufar shirin shi ne wayar da kan al’ummar Najeriya kan mahimmancin tsaftar muhalli a matsayin sahihiyar hanyar shawo kan cututtuka masu yaduwa.domin kare yaɗuwar wannan cuta Akwai hanyoyi daban daban kamar haka: 

Manyan hanyoyin kare kai daga yaɗuwa da cutar ta kwalara shine shawo kan amfani da gurɓataccen ruwa ko abinci .

Tsaftace muhalli musamman wajen cin da kuma dafa abinci , Bayangida,da sauran wurare na aiki a cikin gida

Wanke hannaye kafin cin abinci yana  taimakawa sosai wajen daƙile cutar kwalara a cikin jikin ɗan Adam.

Haka kuma kafin a ci abinci yana da kyau a sake farashi sosai kafin a ci. Ingantacciyyar tsafta na taimakawa wajen daƙile Kwalara

Wanke ƴaƴan itatuwa kafin a kai baki yana da matukar tasiri wajen taimakawa a yaƙi cutar Kwalara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories