Jami’an Tsaro Sun Cafke Mai Safarar Alburusai A Katsina

Jami’an tsaro a jihar Katsina sun kama wata mata mai suna Aisha Abubakar bisa zargin ta da safarar alburusai ga ƴan ta’adda a jihar katsina

 Zagazola Makama Wani mai sharhi kan harkokin tsaro kuma kwararre kan yaƙi da ta’addanci, shi ne ya ruwaito faruwar lamarin a yau Litinin.

 A cewar sa an yi nasarar gano harsashin ne a wani binciken kayan matar da aka yi.

 “Hukumomi sun gano alburusan ne a yayin da ake binciken kayanta” in ji shi

Da farko wacce ake zargin ta musanta aikata safarar , Amma daga baya Zagazola ya ruwaito cewa ta amince da aikata wannan aika aika.

 “Da farko ta musanta amma daga baya ta amsa cewa tana jigilar alburusai ga ƙungiyar ta’addanci daga jihar Nassarawa,” Makama ya bayyana.

Makama ya rubuta cewa, “A yayin da ake yi mata tambayoyi, wacce ake zargin ta amsa cewa ta ɗauki hanyar‘Yan Tumaki a karamar hukumar Dan Musa a jihar Katsina don ta kai kaya.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories