NCDC Ta Kaddamar Da Cibiyar ‘Ko Ta Kwana’ Bayan Kwalara Ta Hallaka Mutane 53 A Jihohi 31

Cibiyar Kare yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta kaddamar da cibiyar ‘ko ta kwana’ ta kasa da shirin daukan matakin gaggawa (EOC) domin dakile yaduwar annobar cutar kwalara da ta bulla a Najeriya.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da Babban daraktan cibiyar NCDC, Dr Jide Idris ya fitar a babban birnin tarayya Abuja ranar litinin, inda ya tabbatar da bullar rahotanni 1528,baya ga mutuwar mutane 53 a jihohi 31 na Najeriya,24 YUNI 2024.

Ya kara da cewa“wadannan rashe rashe ba wai kididdiga ba ne, iyalaai da dama sun rasa ababen kaunarsu, mazajensu, matayensu, iyayensu, da masu bada kulawa ga marasa lafiya.

Ana samun bullar cutar kwalara ne da zarar damina ta fadi an fara samun mamakon ruwan sama”

Daraktan NCDC da yake maida martani ya ce tuni aka tattauna da kwararrun masana kan barkewar cututtuka da sauran masu ruwa da tsaki tun satin da ya gabata don ganin an shawo kan matsalar.

Ya cigaba da cewa tuni aka tuntubi kwararru daga fannoni daban daban(lafiya,  muhalli, noma, albarkatun ruwa da sauransu), ma’aikatu da sauran masu ruwa da tsaki don sanin inda aka dosa wajen ganin an dakile yaduwar cutar tare da kawar duk wata barazanar tasirin cutar.

“Wannan shine ya talista kirkirar cibiyar bada agajin gaggawa ta ko ta kwana dangane da cutar kwalara a fadin kasa baki daya”, a cewar sa.

Daraktan NCDC, ya ce yunkurinsa na bude cibiyar ko ta kwana a kan cutar kwalara ya nuna jajircewa da himmarsa wajen ganin an dakile cigaban barkewar cutar da kuma kula da koshin lafiyar al’ummar Najeriya.

Cibiyar ko ta kwana ta EOC zata kasance masarrafar da za ta kula da dukkan al’amuran da suka shafi cutar kwalar a fadin Najeriya, sannan kuma za ta agazawa jihohin da cutar ta shafa, za ta adana tare yada bayanai, gudanar da kididdiga, yanke shawarwari, da kuma hada hannu da kwararru daga kowanne bangare na sauran masu ruwa da tsaki a kowanne irin mataki na gwamnati.

Ya bayyan cewa zasu tabbatar an wadata cibiyar da duk abin da zata bukata kama daga dakunan gwaje gwaje,kula da ma’aikata, da kuma wayar da kan al’umma domin a gudu tare a tsira tare.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories