Gwamnatin Gombe Ta Dakatar Da Kansila, Hakimi Sakamakon Cefanar Da Tiransfoma

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya amince da dakatar da Hakimin Garin Majidadi da ke ƙaramar hukumar Akko, Mohammed Majidadi

 Sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau.

Hakazalika, Majalisar Karamar Hukumar Akko, bisa dogaro da dokar da ta kafa dokar Karamar Hukumar ta Jihar Gombe, ta shekarar 2013, ta kuma sanar da dakatar da Kansila mai wakiltar Kumo ta Gabas, Abdullahi M. Panda.

 Dakatarwar ta biyo bayan wasu al’amura da suka faru a baya-bayan nan da suka shafi masu muƙamin su biyu,A yanzu haka rundunar ƴan sandan jihar Gombe ta gurfanar da su a gaban kuliya, kuma a halin yanzu suna fuskantar shari’a kan zargin hada baki wajen sata da kuma sayar da tiransifoman Garin Majidadi.

 Haka kuma rahoto ya bayyana cewa Dakatar da mutane biyu wani mataki ne na kariya don tabbatar da cewa ba a tsoma baki yayin Shari’a ba.

Gwamna Inuwa Yahaya, wanda ya jaddada kudirinsa na tabbatar da doka a kodayaushe, ya bayyana cewa lallai za a yi adalci kuma doka za ta yi aiki, Gwamnan ya ƙara da cewa ba kan waɗannan mutane biyu ba duk wani wanda ya yi ba daidai ba zai ga hukunci,kamar yadda sanarwar ta fito daga Ismaila Uba Misilli, Darakta Janar na (Hukumar Yada Labarai), Gombe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories