Da Ɗumi – Ɗumi : Ƴan Bindiga Sun yi Awon Gaba Da Mahaifiyar Mawaƙi Rarara

Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun sace Hajiya Halima Adamu, mahaifiyar shahararren mawaƙin Hausa, Dauda Adamu Kahutu Rarara da misalin karfe ɗaya na daren yau juma’a.

 Hajiya Halima An sace ta ne a gidanta da ke ƙauyen Kahutu a karamar hukumar Danja ta jihar Katsina, kamar yadda wata majiya a kauyen ta bayyanawa Daily Trust.

 “Ƴan bindigan sun shigo ne da ƙafa har cikin gidan inda suka tasa ƙwayar Matar suka tafi da ita.”

Ko da yake ƴan bindigan da suka shigo gidan akwai wasu mutane a tare da ita amma mahaifiyar Rarara kawai suka ɗauka.  Ko da suka tasa kwayar ta babu wani yunƙuri da aka yi dan a hana su domin su na ɗauke da Bindigogi.

 “Muna addu’ar Allah ya dawo mana da ita cikin koshin lafiya domin tana matukar taimaka mana a wannan ƙauyen.  Danta, Rarara yana mana alheri sosai;  ya kawo ci gaba da dama a wannan kauyen domin jin dadin mu.

 Kokarin jin ta bakin fitaccen mawaƙin ta wayar tarho ya ci tura, domin wayoyinsa an yi ta kira ba a ɗaya ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories