Sojoji Sun Damƙe Barayin Karafen Titin Jirgin Ƙasa A Kaduna 

Rundunar Sojan Najeriya , yankin Kaduna ta ce jami’anta sun yi nasarar kama wasu mutane su 47 da ake zargi da satar ƙarafunan titin jirgin ƙasa.

 Mataimakin daraktan riko na sashin, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Laftanal Kanal Musa Yahaya shi ne ya bayyana hakan a yau Asabar a Kaduna.

 Yahaya ya ce, “Sojoji ne suka kama ɓarayin yayin da suke sintiri a Yankin Kakau Daji-Anguwan Ayaba;  sojojin yi nasarar kama mutane 47 da ake zargin barayin titin jirgin kasa ne a ranar 26 ga watan Yuni.”

 Ya ce waɗanda aka kaman an kama su ne sun yi lodin manyan motoci biyu shaƙar da kayan da suka sata .

Yahaya ya bayyana cewa wadanda ake zargin sun bayyana cewa wani Alhaji Babawo shi ne ya dauke su aiki domin su dinga lalata titin tare da dacewa inda su ke kaiwa wani daji dake kusa da titin.

 Ya kuma bayyana cewa an bayyana sunayen waɗanda ake zargin ne a runduna ta 312 ta Artillery Regiment, Kaduna.

 Muƙaddashin kwamandan, 1 Division Provost Group, Laftanar Kanal IY Rena, ya bayyana cewa ana cigaba da bincikar wadanda ake zargin domin a tabbatar da irin barnar da suka yi .

Ya ƙara da cewa, an kuma yi wa waɗanda ake zargin tambayoyi a lokaci mabanbanta , yayin da ake ƙoƙarin ganin an cafke shugaban su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories