Karin Bayani: Jirgi Ne Mai Sarrafa Kansa Ya Yi Hatsari – NAF Ta Yi Karin Haske

Wani jirgin sama mai saukar ungulu mallakar rundunar sojin sama (NAF) ya yi hatsari a yankin karamar hukumar Igabi dake jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne a wani muhalli dake daura da hedikwatar horon sojojin sama dake Mando, karamar hukumar Igabi, kamar yadda gidan Talabijin na Channels ya rawaito.

Mazauna yankin sun shaidawa Channels Television cewa jirgin ya yi hatsarin ne da safiyar ranar Litinin a kauyen Taimi dake kusa da Rigachikun.

Biyo bayan faruwar lamarin, an ga wata tawagar dakarun rundunar sojin sama daga cibiyar su ta 401 da na makarantar koyon tukin jirgi sun isa wurin tare da kebance yankin da abin ya faru domin bayar da agajin gaggawa da kuma binciken abinda ya haddasa hatsarin.

Sai dai, a wani jawabi da rundunar sojin sama ta fitar ta bakin kakakinta, Edward Gabkwet, ta bayyana cewa jrigin da ya yi hatsari ba mai saukar ungule bane, wani jirgi ne na musamman mai sarrafa kansa ba tare da direba ba (UAV).

KARANTA: Dakarun Soji Sun Kashe Gawurtaccen Shugaban ‘Yan Bindiga Kachalla Ragas A Kaduna

Gabkwet ya bayyana cewa, “jirgin rundunar NAF mai sarrafa kansa (UAV) ya samu tangarda yayin da ya ke sararin samaniya domin gudanar da wani aiki. Lamarin ya faru ne a daura da kauyen Rumji mai nisan Kilomita 15 daga sansanin sojin sama.

“Babu batun asarar rayuka tunda jirgin bashi da direba, babu kowa a cikinsa kuma bayan fadowarsa bai ritsa da kowa ba.”

“Tuni an fara gudanar da bincike domin gano abinda ya haddasa hatsarin. Jama’a su kwantar da hankalinsu, wannan karamar tangarda ce da ba zata shafi aiyukanmu ba ta kowacce hanya.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories