Jihohin Arewa 8 Da Ambaliyar Ruwan Kogi Zata Shafa A Watan Yuli – FG Ta Yi Gargadi

Gwamnatin tarayya ta yi gargadin cewa ambaliyar ruwa sakamakon cikar kogi daban-daban dake sassan kasar nan da kewaye zata yi tsanani a karshen watan Yuli, tare da bayyana cewa ambaliyar zata shafi jihohin Najeriya 19 da birnin tarayya, Abuja.

Kazalika, gwamnatin ta yi gargadin cewa ambaliyar ruwan zata kara jawo yaduwar annobar cutar kwalara da ta bulla a wasu jihohi.

Da yake magana da manema labarai a ranar Alhamis, ministan albarkatun ruwa da tsaftarsa, Farfesa Joseph Utsev, ya bayyana cewa tun cikin watan Mayu aka fara samun ambaliyar ruwa sakamakon ruwan sama mai dogon zango da kuma toshewar magudanan ruwa a birane.

Ya kara da cewa, za a fara fuskantar ambaliya mai tsanani a karshen watan Yuli sakamakon cikar Kogi.

Jihohin arewa da ya lissafa cewa ambaliyar zata fi tsanani sun hada da: Benue, Jigawa, Kogi, Kebbi, Kaduna, Niger, Nasarawa, Taraba, da Abuja.

DUBA WANNAN: Ana nuna mana wariya – Gwamnonin jihohin arewa maso gabas sun zayyana matsalolinsu

Sauran jihohin sun hada da Akwa Ibom, Bayelsa, Cross River, Delta, Ondo, Ogun, da Rivers.

Ministan ya bayyana cewa Najeriya tana gangaren kogin River Niger Basin, wanda hakan yasa take yawan fuskantar ambaliya duk shekarar da kogin ya cika sakamakon yawan ruwan sama.

A cewar Ministan, ‘yan Najeriya su zama cikin shirin fuskantar ambaliya a daminar bana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories