Sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken ya isa Najeriya a wani bangare na rangadin mako daya zuwa kasashen yammacin Afirka hudu.
Amurka na fafutukar ganin dorewar tasirinta yayin da take samun gogayya daga ƙasashen Rasha da China.
Kasashe a yammacin Afirka musamman a yankin Sahel sun fuskanci karuwar matsaloli ciki har da sauye-sauyen gwamnatoci a hudu daga cikin mambobin kungiyar ECOWAS 15.
Ziyarar ta zo ne daidai lokacin da Abuja, babban birnin Najeriya ke fuskantar matsalolin tsaro da sace-sacen jama’a.