Wasu rahotanni daga jihar Kano sun bayyana cewa Allah ya yiwa fitacciyar jaruma a Masana’antar Kannywood, Saratu Gidado rasuwa.
Gidan Rediyon Aminci da ke Kano ya bayar da sanarwa jarumar a yau Talata kamar yadda WikkiTimes Hausa ta gani.
Sanarwar ta ce “Allah yayiwa fitacciyar jarumar fina-finan hausa Saratu Gidado ta rasuwa, za a yi jana’izarta da karfe 4:00 na yamma.”
Gabanin ta fara fina-finan hausa shekaru 18 da suka wuce, Saratu Daso malamar makaranta ce. Kuma ta ce aure bai hana ta fim ba. Sannan ta fito a wasu fina-finan turanci.