Zabe:An Dauki Tsauraran Matai A shirye -Shiryen Yanke Hukuncin Kano Da Bauchi

An saka tsauraran matakan tsaro a harabar kotun daukaka ƙara da ke babban birnin tarayya Abuja, yayin da kotun za ta yanke hukunci a kararakin zaɓe da aka shigar na zaɓen gwamnonin jihohin Kano da Bauchi.

Jaridar The Punch Ta ruwaito cewar jami’an rundunar ƴan sandan Najeriya sun killace wasu hanyoyin da ake bi don zzuwa kotun.

Haka kuma an hangi yadda dimbin magoya bayan ke kokarin shiga harabar kotun.

 Wanda hakan ya sanya Jami’an ƴan sanda harba barkono tsohuwa a kokarin su na tarwatsa dandazon magoya bayan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories