Zan Jagoranci Kafa Haɗakar Jam’iyyun Adawa Da Za Su Kawo Ƙarshen Mulkin APC – Atiku

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya bayyana aniyarsa ta jagorantar gamayyar jam’iyyun adawa domin kawar da jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen 2027.

Ya bayyana hakan ne a sakon taya murna ga gwamnonin jam’iyyar PDP da kotun koli ta amince da zabensu a ranar Juma’a.

A wata sanarwa dauke da sa hannun ofishin yada labaransa da ke Abuja, ya bayyana hukuncin kotun a matsayin albishir ga al’ummar jihohin Bauchi, Plateau, Cross River, da Zamfara, kuma hakika nasara ce ga tsarin dimokradiyya.

Haka kuma Atiku Abubakar ya taya gwamnan jihar Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP murna, inda ya jaddada matsayinsa na cewa hadin kan ‘yan adawa ne kadai zai iya karfafa dimokuradiyya a Najeriya.

An jiyo Atiku yana cewa, “Ni a shirye nake kamar yadda aka saba gudanarwa, tare da dukkan shugabanninmu da gwamnoninmu, domin ci gaban kasarmu.”

A cewarsa, “Idan aka ga an yi adalci sosai, mu a matsayinmu na masu kishin kasa da kuma ‘yan kasa, za mu yaba.”

Hakazalika Atiku ya ce, bisa hukuncin kotun koli, “akwai tabbacin ci gaba da gudanar da ayyukan shugabanci nagari da PDP ta kawo a jihohinsu.”

Ya bukaci gwamnonin PDP da suka hada da Bala Mohammed na Bauchi, Dauda Lawal na Zamfara, Barr. Caleb Muftwang na Filato, da Fasto Umo Eno na Akwa Ibom, su ɗauki nasarar da suka samu a kotun koli a matsayin wata dama ta karfafa tare da fadada fa’idar gudanar da shugabanci nagari da suka kafa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories