Na Girgiza Matuƙa Da Kisan Nabeeha A Hannun Masu Garkuwa – Oluremi Tinubu

Mai ɗakin shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu ta bayyana kaɗuwarta kan mutuwar Nabeeha Al-Kadriyar, da ƴan bindiga suka halaka.

A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, Sanata Oluremi ta bayyana mutuwar Nabeeha a matsayin rashi mai matuƙar sosa zuciya inda kuma ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan marigayiyar.

Sanata Oluremi ta kuma buƙaci ƴan Najeriya su haɗa kansu wajen yin addu’oi da za su kai ga sakin ƴan’uwan Nabeeha, waɗanda har yanzu ke a hannun masu garkuwa.

Da take magana kan ƙaruwar matsalar tsaro da sace-sacen jama’a, Oluremi ta yi kira ga hukumomin tsaro su ƙara ƙaimi wajen hana satar jama’a su kuma yi duk mai yiwuwa domin kuɓutar da ƴan’uwan Nabeeha.

A ranar 2 ga watan Janairu Nabeeha da ƴan’uwanta suka faɗa hannun ƴan bindiga a yankin Bwari da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

Mahaifinsu Mansoor Al-Kadriyar, wanda shi ma ya shiga hannun masu garkuwar daga bisani sun sake shi domin ya dawo gida a haɗa kuɗin fansar ƴaƴansa.

Sai dai masu garkuwa sun ƙara kuɗin fansar tare da kashe Nabeeha bayan da aka gaza haɗa kuɗin fansar.

Sun kuma yi barazanar kashe ragowar ƴan matan da ke hannunsu idan aka ƙi biyan su kuɗi kafin wa’adin da suka ɗiba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories