An Tsamo Gawarwaki, Wasu Da Dama Sun Ɓata Sakamakon Hatsarin Kwale-kwale A Neja

Aƙalla mutane takwas aka tabbatar sun mutu inda wasu da dama suka ɓace bayan da wani jirgin ruwan kwale-kwale dauke da sama da mutum 100 ya kife a arewa maso-yammacin Nijeriya a ranar Talatar nan.

Hatsarin ya afku a ranar Litinin a jihar Neja a yayin da jama’ar kauyen Dugga suke tafiya kasuwa a jihar Kebbi mai maƙwabtaka da su don sayar da hatsi da rake.

Ana yawan samun hatsarin jiragen ruwa a kogunan Nijeriya, kuma ana yawan dora alhakin lamarin kan lodin da ya wuce ƙa’ida da rashin gyara jiragen ruwa akai-akai.

Ibrahim Hussaini, kakakin Hukumar Agajin Gaggawa ta jihar Neja ya ce sauyin kadawar iska da aka samu nan take ne ya kifar da jirgin da aka yi wa lodin da ya wuce ka’ida.

Hussaini ya kara da cewa an tsamo gawarwaki takwas yayin da aka kubutar da mutane biyar da rayuwakansu, ana kuma ci gaba da neman wasu da dama da suka bata.

Daraktan Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Neja Ibrahim Audu ya bayyana cewa diban mutane da kayan da suka wuce ƙa’ida ya taimaka wajen afkuwar hatsarin jirgin ruwan.

Ya ce jiragen ruwan da suke da ikon daukar mutane 100, amma ana loda musu sama da haka da kuma kaya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories