Bom Ya Tashi A Tsakanin Wasu ‘Almajirai’ A Jihar Kaduna

Wani bom da ya fashe a ƙauyen Kidandan da ke yankin ƙaramar hukumar Giwa a jihar Kaduna ya yi sanadin mutuwar wani dalibin makarantar Islamiyya yayin da wasu goma suka samu raunuka kamar yadda jaridar Premium Times ta rawaito.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Kaduna, Samuel Aruwan, a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, ya ce jami’an tsaro na gudanar da bincike a kan fashewar bom ɗin.

Aruwan ya ce, “A cewar rahotannin farko da aka samu daga ƙauyen da kuma jami’an tsaro, ɗaya daga cikin ɗaliban da ke karatu a ƙarƙashin wani malamin garin ya dauko wani abu daga daji, wanda daga baya ya fashe a tsakanin ƴan uwansa ɗalibai.”

Ya ce ya zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar almajiri ɗaya mai suna Zaidu Usman, yayin da wasu kimanin 10 suka samu raunuka kuma suna samun kulawa a asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika-Zariya.

Aruwan ya ce, “Gwamna Uba Sani na jihar ya samu rahoton cikin kaduwa da bakin ciki, sannan ya aika sakon ta’aziyya ga wadanda abin ya shafa da iyalansu, inda ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu, ya kuma basu lafiya.”

Ya ce gwamnan ya kuma yi kira ga iyaye da shugabannin al’umma da su kara sanya ido kan ayyukan ‘ya’yansu a koda yaushe domin guje wa irin haka a gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories