Kotun Ƙolin Najeriya Ta Tabbatar Da Ɗaurin Shekaru Biyar A Gidan Yari Ga Farouk Lawan

Kotun Kolin Nijeriya ta tabbatar da hukuncin zaman gidan yari na shekara biyar ga tsohon ɗan majalisar wakilai mai wakiltar ƙananan hukumomin Bagwai da Shanono a jihar Kano, Farouk Lawan, bayan tabbatar da laifin karɓar cin hancin dala 500,000 daga fitaccen ɗan kasuwan nan Femi Otedola.

A yau Juma’a ne Mai Shari’a Tijjani Abubakar na kotun ya karanto hukuncin inda ya kori ƙarar da Farouk Lawan ya ɗaukaka kan hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke a watan Fabrairun 2022.

A ranar Talata 23 ga watan Yunin 2021 ne wata Babbar Kotu a Najeriya ta zartar da hukuncin ɗaurin shekaru bakwai kan Farouk Lawan, tsohon shugaban kwamitin tallafin mai a majalisar wakilan kasar nan.

Tun da farko an zargi Farouk Lawan ne da karɓar dala dubu 620 daga hannun Mista Otedola, a lokacin da shi Farouk din yake shugabantar kwamitin binciken badaƙalar kuɗaɗen tallafin mai a shekarar 2012.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories