Shin Zunubinmu Ne Yake Hanamu Yin Arziƙi?

Na sha cin karo da wata shubuha da ake yadawa cewa wai idan da zunubin mu ne yake hana mu arziki me yasa Dubai da sauran kasashen larabawa, wadanda su ma suna yin fiye da namu, suke da arziki? Babu alakar zunubin mu da talaucin da muke ciki, rashin iya kasuwancin mu ne ko rashin aiki da dabaru.

Ma’ana dai kada a bar zunuban a ci gaba da su, indai don kudi ne to a nemi ilimin iya kasuwanci, komai zunubin ku za ku samu kudi.

To in aka samu kudin kuma fa, daga nan sai me? Zunuban sun zama ba za su kai mu wuta ba kenan? Idan zunubi zai kai mu wuta to menene dadin duniyar? Kudin za su hana mana bakin ciki ne a duniya, ko za su tabbatar mana da rayuwa babu kowacce matsala? Shin za su hana yaran mu lalacewa da shaye-shaye ko kuwa za su kore mana dukkan matsaloli?

Ai ba ma kasashen musulmi ya kamata a ba da misali ba, cewa suna yin zunubi amma sun samu arziki. Ga kasashen kafirai nan ma? Duk ba sun fi na Musulmin karfin tattalin arziki ba? Maimakon mu daina damuwa da zunubi don ba zai hana mu talauci ba, ai kafircin ma misali ne na cewa baya hana arziki? To don kafirai suna da arziki, duk da kafircin su, shi ke nan kada mu guje shi kenan?

To yanzu, tunda yawan samun kudi ne ma’aunin ku na cewa zunubi ba abin gudu ba ne, tunda ba ya hana talauci, shin kuna nufin guje wa yin zunubin ne yake kawo talauci? Idan gujewa yin zunubin ne yake kawo talauci me yasa Kano da ake gujewa giya ake yakar fasadi a bayyane ta fi Ebonyi arziki? Me ya sa ake samun kasashen da suke kaucewa zunubin kuma sun fi wadansu wadanda ba sa kaucewar arzikin?

Al’ Kur’ani ya yi mana bayanin yanda akan sakarwa fajirai duniya domin su dada shagala, sai sun saki jiki Allah ya ragargaje su. Don haka ganin wasu kasashe, ko da na Musulmi ne masu sabo, suna cikin daular duniya ba zai rude mu cewa mu ma mu saki jiki da sabon ba.

Har ma Allah yana nuna mana cewa yana sakarwa kafirai duniya ne domin ya azabtar da su da ita. Don haka ganin wani wanda ba ya bin Allah ya samu dukiya ba zai taba zama wata hujjar da za a ce to musulmi su daina ma damuwa da sabo ba, tunda ba ya hana samun arziki.

A wajen Musulmi, samun dukiya ba ma’auni ba ne. Shi ya sa Annabi ya ce “Idan da duniya tana da kimar fiffiken sauro, to da ko makwarwar ruwa daya kafiri ba zai samu ba a cikin ta.”

Shin ba kwa mamaki? Za a iya bayar da misali da cewa ba cin hanci ne ya hana mu ci gaba ba, tunda akwai kasashen da ake cin hanci amma sun ci gaba. Za a iya misali da yawan jama’a, tun da ga kasashe nan da suke da yawan jama’a kuma sun ci gaba, kamar Indiya da China. Za a iya bayar da misali da rashin yin dumkradiyya, tun da ga kasashe nan da ba sa yin dimukradiyya kuma sun fi mu arziki, kamar kasashen larabawan. Za a iya misali da rashin mulkin mace, tun da ga kasashe nan kamar Amurka da mace bata taba mulki ba kuma sun ci gaba.

To me ya sa sai zunubi ne kawai za a damu don mun guje masa? Saboda idan sabo ya yadu a cikin mu za mu dada lalacewa mu zama irin yanda makiyan mu suke so mu zama.

Muna kaucewa zunubi ne saboda Allah ya hana, ba don kada mu yi talauci ba.

Muhammad Mahmud ya rubuto daga Kano – Najeriya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories