Ra’ayi: Hauhawar Farashin Kayan Masarufi Laifin Gwamnati Ne

Idan al’amuran kasa suka tabarbare sai a rasa waye mai laifi. Hukuma ta zargi yan kasuwa, yan kasuwa su zargi hukuma. Talaka ya zargi kowa. Amma maganar gaskiya lamarin nan fa matsalar gwamnati ce da masu madafin iko kaso casa’in cikin dari.

Yan kasuwa fa kokari suke kawai su tattala jarinsu kada ya ruguje a wannan yanayi na dari dari. Alal misali, yau kaje kamfani ka saro shinkafa akan buhu naira 50000, kai kuma ka sayar 50500 ka samu ribar 500 akan kowanne buhu. Ka fara sayarwa kenan sai kamfani ya mayar da ita buhu naira 53000. Idan ka cigaba da sayarwa akan 50500 maimakon riba yanzu asara kake yi ta 2500 akan kowanne buhu. Domin idan zaka saro wani kayan nan gaba jarin ka ba zai iya saya maka adadin da kake saya a baya ba.

İrin wannan yanayin da ake ciki yafi tayarwa da yan kasuwa hankali. Saboda babu market stability baka san ma ko riba kake ci ko faduwa ba. Jarin da zai saya maka buhu dari, a sati guda ya koma buhu 70 kawai zaka iya saya da shi. Kafin kace kobo, jari yana neman karyewa.

A dan takaitaccen lokaci gwamnati ta cire tallafin manfetur, ta karya darajar naira, ta lillinka import duty, ga shi tana shirin kara VAT zuwa 10%- ta yaya kasuwa baza ta rikice ba? Sannan ga shi taaddanci da garkuwa da mutane, hadi da karancin ruwan sama sun sa noman da akai a shekarar bara bai kai ya kawo ba. A hakan gwamnati bata yarda a shigo da abinci daga border ba.

Tsaretsaren gwamnati suna da tasiri ga yanayin da muke ciki. Muddin gwamnati ba zata sassauta al’amura ba, za ayi ta zargi da zaluntar yan kasuwa bada hakkinsu ba. Za ayi ta fasa musu stores ana karya musu jari. A karshe ayi haihuwar guzuma- da kwance, uwa kwance.

Dr Ibrahim Musa likita ne Kuma Mai sharhin al’amuran yau da kullum

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories