Sojoji Sun Lalata Maɓoyar Ƴan Bindiga, Sun Ceto Waɗanda Aka Yi Garkuwa Da Su A Taraba

Dakarun Bataliya ta 114 (Rear) na 6 Brigade, rundunar sojojin Najeriya tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro a ranar Asabar sun yi nasarar lalata maɓoyar yan bindiga da dama tare da ceto wasu mutane 4 wɗanda aka yi garkuwa da su a karamar hukumar Yorro a jihar Taraba.

 Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Laftanar Olabodunde Oni, muƙaddashin Daraktan hulɗa da jama’a na rundunar soji ta 6, wanda ya sanarwa manema labarai a Jalingo a ranar Lahadi.

 Muƙaddashin Ya bayyana cewa an fara ɗaukar matakin gaggawa na fatattakar ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane waɗanda ke kawo cikas ga zaman lafiya a garin na Yorro da ma kewayen ta tun a ranar 2 ga watan Fabrairu.

Ya ce sojojin sun yi arangama da ‘yan bindigan ne a tsaunin Gampu da kuma yankin Ban Yorro inda suka sake musu wuta wanda hakan ya sa ƴan bindigar suka tsere , su ka bar mutane huɗu da suka sace.

 “Har yanzu ana ci gaba da gudanar da kai simamen domin tabbatar da ganin an gano sauran waɗsnda aka yi garkuwa da su da suka gudu daga yankin a yayin musayar wuta don miƙa su ga ƴan uwansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories