Yau Take Ranar Yaƙi Da Ciwon Daji Ta Duniya

Ranar 4 ga watan fabrairun kowace shekara rana ce da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ware a matsayin ranar fadakar da jama’a a kan illar cutar cancer ko daji ga bil’adama.

Manufar dai ranar ita ce, karawa jama’a fahimta dangane da cutar ta Cancer da kuma kawar da duk wasu tunani dake da nasaba da al’ada dangane da wannan cuta mai hallaka jama’a.

Hukumar lafiya ta duniya, wato WHO ta ce, cutar ta Cancer ce kan gaba wajen hallaka jama’a a duniya, kuma ta ce, koda a shekara ta 2008 cutar ta hallaka mutane fiye da miliyan bakwai.

A ƙasashen Afurka wannan cuta ta Daji na hallaka jama’a da dama saboda dalilai da dama da suka hada da rashin gano ta akan lokaci da kuma rashin kayan aiki a asibitoci domin kula da masu fama da cutar da kuma tunani iri iri masu nasaba da al’ada dangane da wannan cuta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories