Ƴan Bindiga Na Barazanar Kawomin Hari – Dikko Radda

Gwamnan jihar Katsina da ke Arewacin Najeriya, Malam Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa ƴan bindiga da su ka addabi jihar sun yi barazanar kai masa hari.

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokaci. wani taron gaggawa na majalisar tsaro da aka yi a gidan gwamnati.

Ya ce ya samu bayanin barazanar ƴan bindigar ne daga rahotannin tsaro.

“A bisa rahotannin tsaro da muke samu, ina cikin waɗanda ƴan bindigar ke tunanin kai hari, amma hakan bai sa na karaya ba, domin Allah yana tare da mu, kuma zai kare mu.”

Sai dai gwamnan ya bayyana cewa barazanar da ‘yan bindigar ke yi ba zai hana gwamnatin sa daukar sabbin dabarun tsaro na magance ‘yan fashin daji da sauran matsalolin tsaro a jihar ba.

Idan za a iya tunawa dai Dikko Umaru Radda, ya taɓa bayya cewa zai iya sadaukar da rayuwarsa domin kawo karshen matsalar ‘yan bindigar da suka addabi jihar Katsina.

Matsalar rashin tsaro na ci gaba da addabar sassa da dama na jihar Katsina sakamakon ayyukan ‘yan bindiga, wadanda ke cin karensu babu babbaka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories