Duk Wahalhalun Da Ƴan Najeriya Su Ke Ciki Buhari Ne Sanadi – Tsohon Sarkin Kano Sanusi

Tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ya dora alhakin wahalar da ƴan Najeriya ke ciki a kan tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Sanusi ya ce ba adalci ba ne a zargi shugaba Bola Tinubu kan wahalhalun da ‘yan Najeriya ke ciki.

Muhammadu Sanusi II ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a lokacin da ya ke jawabi taron addinin da ya gudana a kafar intanet. Ya ce tsohuwar gwamnatin Buhari ta gaza bin shawararsa kan yadda za a ceto Najeriya daga matsalolin tattalin arziki.

Tsohon Sarkin ya kuma sha alwashin sukar Tinubu idan ya ga wata manufar tattalin arzikin da ba ta dace ba a nan gaba.

A cewar Sanusi: “Idan zan yi adalci kuma in yi wa Shugaba Bola Tinubu adalci, ba shi ne ya jawo wahalhalun da ake ciki a yanzu ba; tsawon shekaru takwas, muna rayuwar ƙarya tare da bashi mai yawa daga basusukan waje da na cikin gida.

“Ba zan iya shiga cikin sauran ƴan Najeriya da ke sukar Tinubu kan matsalar tattalin arziki da ake ciki a halin yanzu ba, kuma ba wai ina cewa shi waliyyi ne da ya kubuta daga aikata ba daidai ba, amma a halin da ake ciki na tattalin arzikin da ake ciki, ba za a zargi Shugaba Tinubu ba.

Haka kuma tsohon Sarkin ya ce babu wata mafita face cire tallafin man fetur a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories