Dala Ta Yi Tsadar Da Ba A Taɓa Ganin Irinta Ba A Tarihin Najeriya

A karon farko, dala guda ta zarta naira 1,500 a farashin gwamnatin Najeriya, abin da ke nuna cewa, babu alamar kawo karshen matsalar tsadar dala a kasar.

A jiya Litinin, an sayar da dala guda a kan naira 1,534 a farashin gwamnati a daidai lokacin da ‘yan kasar ke ci gaba da koka kan tsadar rayuwa da aka alakanta ta da tsadar dalar.

Wannan kuwa na zuwa ne duk kuwa da matakan da babban bankin kasar na CBN ke cewa yana dauka na ganin ya kassara farashin dalar domin daidaita kasuwar hada-hadar kudaden ketare.

Sai dai har yanzu darajar nairar ta ci gaba da rugujewa, yayin da dalar ke ci gaba da hauhawa.

Tuni wannan matsalar ta haddasa tsadar abinci da magunguna da sauran kayyakin da ake shigowa da su cikin Najeriya.

Ko da yake wasu bayanai na cewa, ana sayar da dalar a tsakankanin farashin naira 1,450 zuwa 1,500 a kasuwannin bayan-fage.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories